⁠Koyon Hada Jaka (Basics of Bag Making)

Ka gaji da sayen jaka? ka gaji da fidda kuɗi ka sayi jakunkuna ka rabar lokacin biki ko suna? A wannan darasin za ku koyi yanda ake haɗa jaka da purse kala-kala cikin sauƙi da kuma kaya kaɗan. Jaka na daga cikin abubuwan da mata ke ado da shi hakazalika yana ƙara wa ado armashi, hasali ma za a iya cewa mace in bata cika adonta da jaka ko purse ba bata yi fita na girma ba. Ku bi wannan darasi don samun sauƙin kuɗaɗenku.

Watch the Trailer

Write your awesome label here.

Abunda Ke Kunshe A Ciki

  • Bidiyo na kallo guda 6
  • Jarrabawa 
  • Takardar Kammalawa

Game Da Wannan Darasin 

A wannan darasin zamu duba yanda mutum zai cigaba da bunkasa rayuwar sa ta koyan aikin hannu, sana'a, kwaikwaiyar dabi'u masu kyawu tare da yin taka tsantsan da muradun su na rayuwa domin cimma nasara a rayuwa.

Fahimta

A wannan darasin za ku koyi yanda ake haɗa purse har kala uku, da kayan aiki a sauwaƙe da kuma yan kaɗan.

Darussan da ke Ciki

GA MALAMAR KU

Khadija Hamma Umar

Khadija Hamma Umar ɗalibar makaranta ce a jami'ar Usman Dan Fodio, tana karantan Pharmacy. Ta koya haɗa jaka ne a wani hutu da ta zo har ya zama sana'arta yanzu.

Ta zo muku da wannan darasin ne domin kuma ku koya yanda ake haɗa jaka ta yanda zaka iya yi da kanka ba tare da ka biya kuɗi masu yawa wajen siya ba.